Ba musuluntar da Najeriya za a yi ba - JNI

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption JNI ta ce ba ta ga dalilin da zai sa wasu su ce an tauye musu hakki na shiga hadakar yaki da ta'addanci ba

Kungiyar musulmin Najeriya ta Jama'atu Nasril Islam ta ja hankalin kiristocin kasar kan damuwar da nunawa game da shigar da kasar cikin kawancen kasashen Musulmi da za su yaki kungiyoyin ta'addanci a duniya da aka ce gwamnatin kasar ta yi.

Kungiyar ta Jama'atu Nasril Islam, wadda ita ce babban kungiya ga al'ummar Musulmi a kasar, ta ce ba ta ga dalilin da zai sa wasu su ce shiga hadakar ta yaki da ta'addanci ta tauye musu hakki ba.

Sakatare Janar na kungiyar, Dr Khalid Aliyu ya shaida wa BBC cewa Najeriya ta dade tana da kyakkyawar danganta da kasashen Musulmai har ma da kasashen Kiristoci, a don haka bai kamata kiristocin su yi Allah-wadai da matakin shigar da kasar cikin kawancen kasashen Musulmi don yaki da ta'addanci a duniya ba.

A karshe mako ne dai Dattawan kungiyar kiristoci na Najeriya suka yi Allah wadai da matakin da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta dauka na shiga kawancen kasashen musulmi da za su yaki kungiyoyin 'yan ta'adda a duniya.

A wata hira da BBC Dr. Saleh Husseni na dattawan kungiyar kiristocin, ya ce bai kamata a shigar da Najeriya cikin kawancen ba da kuma yunkurin karbo ba shi da gwamnatin kasar ke yi daga Bankin Musulunci ba.