Togo: Ana hatsaniya kan zaben Niger

Image caption 'Yan Nijar na da ikon kada kuri'a a kasashen waje a karkashin kulawa ofisoshin jakadancin kasar.

Rahotanni daga Lome babban birnin Togo na cewa an yi hatsaniya a wasu runfunan zabe inda 'yan Nijar ke kada kuri'a a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa.

Ministar harkokin wajen Nijar Madam Kane Aichatou Boulama ta tabbatar wa BBC faruwar lamarin, amma ta ce kura ta lafa.

Ta kuma kara da cewa an Kame mutane 22 da ake zargi, ciki har da wadanda ba yan Nijar ba.

Dama da hukumomin Nijar sun bai wa 'yan kasar da ke zaune a kasashen waje damar jefa kuri'a a inda suke .