Ana cigaba da tattara sakamakon zaben Nijar

Image caption An dai kwashe daren Litinin ana kidayar kuri'a.

A jamhuriyra Nijar, hukumar zaben kasar ta yi nisa wajen tattara sakamakon shugaban kasar zagaye na biyu da aka gudanar a jiya.

Yan adawa dai sun kaurace wa zaben, suna zargin magudi a zagaye na farko na zaben, da kuma yadda suka ce ana takura wa dan takararsu Hama Amadou, wanda yanzu haka ke kasar Faransa yana jinya, bayan da lafiyarsa ta tabarbare a gidan yari.

Wakilan BBC da ke jamhuriyar ta Niger sun ce an yi amfani da fitilar tocilan wajen samar da haske yayin kidayar a wasu ciboyoyin zaben.

Maitaimakiya ta biyu Ta shugaban hukumar zaben mai zaman kanta, watau CENI, Maryama Katambe, ta ce an cigaba da gudanar da zabe duk da cewar, 'yan adawa sun ce sun janye.

Ta kara da cewa tunda dai dan takarar adawan bai janye ba dole ne suyi aikinsu. Kuma suna kyautata zaton zuwa gobe da safe za a ida kidaya kuri'un.

Masu sa idanu kan yada zaben ke gudana dai sun ce babu alamun matsala, duk da cewar jama'a basu fito sosai ba.