Yau ake zabe a kasashe shida a Africa

Image caption Ana kada kuri'a a kasashe daban-daban a ranar Lahadi a Africa

Yau ranar Lahadi ce mai muhimmanci a Africa, domin ranar ce wacce da ake gudanar da zabe a kasashe shida a nahiyar.

A yau ne ake zaben shugaban kasa a Congo-Brazzaville, a jamhuriyar Nijar da Benin da kuma Zanziba, zabukan shugaban kasa a ke yi zagaye na biyu, a Cape Verde kuwa zaben 'yan majalisun dokoki a ke yi.

'Yan Senegal kuwa na kada kuri'ar raba gardama ne na amincewa da wasu sauye-sauye a kundin tsarin mulkin kasar, ciki har da rage wa'adin shugabancin kasar.

A Congo, an canza kundin tsarin mulkin kasar a shekarar da ta wuce don ba shugaban kasar Denis Sassou Nguesso, wanda ya dade akan mulki, ya yi tazarce.