Turkiyya ta zargi IS da kai harin Istanbul

Hakkin mallakar hoto AP

Hukumomin Turkiyya sun ce wani dan kunar bakin wake wanda ke da alaka da kungiyar IS shine ya kai harin da ya auku a Istanbul.

Sun ce an kama wasu mutane biyar dangane da harin wanda aka kai a wani mai cike da hada hadar jama'a a tsakiyar birnin.

Mutane hudu suka mutu a harin da dan kunar bakin waken Mehmet Ozturk wanda dan Turkiyya shi ma ya rasa ransa.

Uku daga cikin mutanen da suka rasu a harin yan Israila ne kuma kasar ta shawarci jama'arta su kiyayi tafiya zuwa Turkiyya.

Babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin.