Apple ya fitar kananan iPhone da iPad Pro

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption iPhone SE waya ce da ake iya sarrafa ta da kuma haruffan rubutun ta dai dai ya ke da babbar wayar Apple 6S

Kamfanin Apple ya fitar da kananan wayoyin iPhone da iPad Pro a wani taro da aka gudanar da San Francisco wanda aka watsa kai tsaye ta internet.

Samfurin wayar iPhone SE waya ce da hanyoyin da ake iya sarrafa ta da kuma haruffan rubutun ta dai dai ya ke da babbar wayar Apple 6S, kuma ta na iya daukar vidiyo mai girmar 4K.

Sabuwar iPad Pro nada allo da girman ta ya kai inci 9.7 dai dai da ainihin iPad.

Kamfanin ya ce za'a fara sayar da sabuwar wayar ta iPhone SE a kasashe 110 nan da karshen watan Mayu.