Arsenal na horar da yaran Iraki a kan kwallo

Image caption Kulob din Arsenal na da arzikin da zai iya tallafawa yara 'yan gudun hijira

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal tana bai wa yaran da suka tserewa yakin Iraki horo kan wasan kwallo, tare da hadin gwiwar kungiyar Save the Children, inda suka gina filayen wasa a sansanonin 'yan gudun hijira.

Kyaftin din kungiyar mata ta Arsenal Alex Scott ce take jan ragamar bayar da wannan horo ga horo.

Idan aka kwatanta tashin hankalin da yaran suka samu kansu a dalilin yaki da kuma dumbin arzikin da kungiyar ke da shi, za a ga cewa hanyar mota daban da ta jirgi.

Daya daga cikin yaran Esra, ta tsere ne daga garinsu da ke kusa da Bagadaza lokacin da rikicin kasar ya shiga garin nasu.

Ta ce, "A gidanmu akwai katon fili da muke wayataywa ni da 'yan uwana da iyayena, amma yanzu muna rayuwa a sansanin da ke cike da mutane fiye da 6,000."

Alex Scott ta ce, duk da cewa an san wasan kwallo ba shi ne zai mayar da su gidajensu ba, amma ana saran zai sa musu farin ciki a rayuwarsu ta sansanin