Benin: Firaiminista ya yadda ya fadi zabe

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaban jamhuriyar Benin, Boni Yayi tare da shugaban Faransa, Francoise Hollande.

Farai ministan jamhuriyar Benin, Lionel Zinsou, ya yarda cewa ya fadi zaben zagaye na biyu da aka yi ranar Lahadi.

Mista Zinsou ya rubuta hakan ne a shafinsa na Facebook, har ma ya ce ya kira abokin takararsa Mista Patrice Talon, domin ya taya shi murna.

Mista Talon wanda ake sa ran zai maye gurbin mista Zinsou dai hamshakin dan kasuwa ne a kasar, kuma ana yi masa lakabi da 'sarkin auduga'.

Shugaban kasar mai barin gado Thomas Boni Yayi, zai bar karaga bayan kammala wa'adi biyu.

A ranar Litinin ne dai ake sa ran hukumar zaben kasar za ta sanar da sakamakon zaben.