BH: Ko kasan asarar da aka yi a Borno?

Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption Wata kasuwar shanu da ke cin wuta a Najeriya.

Rahotanni daga Najeriya na cewa Jihar Borno ta arewa maso gabashin kasar ta yi asarar dala biliyan biyar da miliyar dari tara sakamakon rikicin Boko Haram.

Jaridar Daily Trust ta kasar dai ta ambato wani rahoto na Bankin Duniya yana kididdige asarar da aka yi tun shekarar 2009, lokacin da kungiyar ta Boko Haram ta fara ta da kayar baya.

Wata majiya ta gwamnatin Borno dai ta tabbatar wa BBC cewa dala biliyan bakwai ne lissafin da jihar ta tura wa Bankin Duniyar a matsayin asarar da aka yi.

Jihohin yankin arewa maso gabashin kasar dai na tattara alkaluman asarar da suka yi ne a matsayin wani bangare na shirin sake gina yankin bayan kawo karshen ta da kayar baya.