Congo: ICC ta samu tsohon shugaba da laifi

Hakkin mallakar hoto
Image caption Jean-Pierre Bemba shi ne tsohon shugaban kasar Congo, kuma kotun ICC ta same shi da laifin aikata laifukan yaki da cin zarafin bil adama.

Kotun duniya mai hukunta miyagun laifuka ICC ya samu tsohon shugaban kasar Congo, Jean-Pierre Bembe da laifin laifukan yaki da cin zarafin dan adam.

A hukuncin da ta yanke, kotun ta ce Mista Bemba ne ke da alhakin yin kisa da fyaden da dakarun sa suka yi wa jama'a, a Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya, shekaru 10 da suka gabata, lokacin yana jagoran 'yan tawaye.

Alkalin kotun ta ICC a Hague, ya ce Mista Bemba, yana da cikakken iko a kan dakarunsa, amma bai tsawatar musu ba, lokacin da suke aika-aikar.

A jawabin da ta yi a wajen kotun, babbar sakatariyar kungiyar MLC ta Mista Bemba, Eve Bzaiba ta ce bai kamata a dora mushi duka laifukan ba.