Abubuwa 5 da ya kamata ku sani kan Cuba

Shugaban Amurka Barack Obama ya isa Cuba a wata ziyara mai cike da tarihi da kuma tattaunawa da shugaban kasar.

Shi ne shugaban Amurka na farko da ya kai ziyara Cuba tun bayan juyin juya halin da aka yi a shekarar 1959, wanda ya jawo lalacewar dangantaka tsakanin kasashen ta shekaru da dama. BBC ta yi duba kan abubuwa biyar da ku ke bukatar sani game da tsibirin na Cuba.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mista Obama na ziyarar kwanaki uku a Cuba

1. Yawan al'ummar kasar Cuba ya kai fiye da miliyan 11, kuma yaren Sifaniya ne harshen da aka fi amfani da shi, addininsu kuma kiristanci ne. Tsawon shekarun da maza ke kai wa shi ne 77, yayin da mata kuwa ke kai wa har 81.

2. Gwamnatin kwaminisanci ta Cuba ta kai shekara 50 tana karkashin takunkumin Amurka wanda aka sanya da niyyar hambarar da gwamnatin shugaba Fidel Castro.

Ta kuma bujirewa hasashen cewa ba za ta kai labari ba sakamakon rugujewar mai goyon bayanta wato Rasha. Sai dai wannan ziyara bata nufin gyaruwar alakar ne gaba daya.

Takunkumin tattalin arzikin da Amurka ta sanyawa Cuba tawon sheakara 54 har yanzu ba a cire shi ba, kuma za a iya cire shi ne kawai idan majalisar Amurka ta kada kuri'a.

Kazalika, har yanzu Cuba tana korafi kan mamayewar da sojin ruwan Amurka suka yi a Guantanamo Bay.

3. Tun bayan faduwar shugaban mulkin kama karya da Amurka ke goyon baya Fulgencio Batista, a shekarar 1959, Cuba ta zama kasa mai jam'iyya daya karkashin jagorancin Mista Castro - tun watan Fabrairun 2008.

Fidel Castro ya kawo juyin juya hali Cuba a shekarar 1950 ya kuma kirkiri kasar kwaminisanci ta farko a yamma.

Image caption Yayin ziyarar tasa shugaba Obama zai kuma sadu da 'yan tawayen kasar

4. Gwamnati ce take da cikakken iko da kafofin yada labarai na Cuba kuma dole ne 'yan jarida su yi aiki bisa dokokin gwamnatin ba tare da cin zarafinta ba, wanda yin hakan zai iya kai mutum zaman gidan kaso na skekaru uku.

A farkon shekarar 2006 ne manema labarai na kungiyar Reporters without Borders suka bayyana Cuba a matsayin "daya daga cikin kasashen da suka fi munin zama ga 'yan jarida da masu rubutu a intanet, suke kuma yawan fuskantar matsin lamba."

5. A shekarar 2013 ne mawaki Jay-Z ya kare ziyarar da ya kai Cuba a wata wakarsa da ya yi mai kamar budaddiyar wasika, bayan da wasu 'yan siyasa biyu suka tambayi dalilin ziyarar tasa zuwa kasar shi da matarsa Beyonce.

An tambayi jami'an Amurka ko an bai wa ma'auratan damar ziyara. Ba a barin 'yan Amurka zuwa Cuba a matsayin yawon bude ido, amma a kan basu lasisi na shiga kasar da zummar karatu ko addini ko kuma tafiyar musayar al'adu.

Fadar Amurka ta ce shugaba Obama da kansa bai bayar da izinin tafiyar Beyonce da mijinta Jay-Z zuwa Cuba ba. Amma jami'an baitul malin Amurka sun ce an basu lasisin tafiyar musayar al'adu ne.