Niger 2016: Ra'ayoyin mutane kan zabe

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan kasar Nijar sun bayyana mabambamtan ra'ayoyi a kan takaddamar zaben shugaban kasar zagaye na biyu

A ranar Laraba dai ake sa ran hukumar zabe ta jamhuriyar Nijar watau CENI, za ta bayyana sakamakon karshe na zaben shugaban kasar zagaye na biyu wanda ake jin shugaba Muhamadou Issoufou ne zai lashe.

'Yan adawa dai sun kaurace wa zaben, suna zargin magudi a zagaye na farko na zaben, da kuma yadda suka ce ana takura wa dan takararsu, Hama Amadou wanda yanzu haka ke kasar Faransa yana jinya, bayan da lafiyarsa ta tabarbare a gidan yari, kuma 'yan adawar na cewa ba zasu amince da sakamakon zaben ba.

A halin da ake ciki dai ana tayar da jijiyoyin wuya tsakanin bangaren gwamnati da na 'yan adawar, yayin da ake halin rashin tabbas kan makomar siyasar kasar.

Wakilinmu Is'haq Khalid ya jiyo mana ra'ayoyin wasu talakawa 'yan Nijar din a birnin Niamey kan wannan takaddama, ga kuma ra'ayoyin na su.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti