Nigeria za ta fadada hanyoyin samun kudi

Image caption Shugaba Buhari ya ziyarci kasashen duniya da dama don tattaunawa kan tattalin arziki

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya yi kira ga bankuna da su kara taimakawa wajen bayar da rance ga bangaren noma, a wani kokari da gwamnati ke yi na farfado da tattalin arzikinta sakamakon faduwar farashin man fetur.

Wannan yunkuri ya biyo bayan kokarin da shugaba Buhari ke yi na ganin ya samar da wasu hanyoyin samun kudin shiga baya ga bangaren man fetur.

Shugaba Buhari ya shaidawa majalisar tattalin arzikin Najeriya cewa, "Babbar hanyar arzikinmu ita ce noma da kiwo."

Ya kara da cewa, "Don haka dole bankuna su kara yawan kudaden da suke bai wa manoma rance. Kuma babban bankin kasa zai kasance mai bayar da lamuni na basussukan a matsayin tsarin kasa."

Kazalika shugaban Najeriyar ya ce gwamnatinsa na shirin kara megawat 10,000 na wutar lantarki a kasar nan da shekaru uku da suka rage masa a kan mulki.

Faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya ya jawo tabarbarewar tattalin arzikin Najeriya.