'Masu ba da umarni su ne kashin bayan fim' —Yasin

Image caption Hafizu Bello na daya daga cikin masu ba da umarni a Kannywood

Masu ba da umarni a Kannywood din sun ce harkar a bunkasa a sakamakon horon da suke samu da kuma bincike da suke kara zurfafawa.

A hirar su da BBC Auwal Yasin ya ce, shi ne ya ba da umarni a fim din da Sadik Sani Sadik a ya ci gwarzon jaruman fina-finan Hausa na shekarar 2015.

Auwal ya kara da cewa "sune kashin bayan duk wata nasara da ake samu a harkar".

A wata hirar da Hafizu Bello ya yi da BBC a yayin ziyarar su Amurka ya ce, sun samu horo a harkar da za ta taimaka wa fina-fina na Hausa su ci gaba.

Sai dai har yanzu ana zargin fina-finan da bata tarbiyya, zargin da 'yan fim din ke musantawa.