Wace rawa Twitter ta taka a rayuwarka?

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Evans William, daya daga cikin mutane hudun da suka kafa Twitter, shekara 10 da ta wuce.

A ranar Litinin din nan ce kafar sada zumunta ta Twitter ta cika shekara 10 da kafawa.

A ranar 21 ga Maris na 2006 ne dai wasu matasa guda hudu wato Evan Williams da Noah Glass da Jack Dorsey da kuma Biz Stone suka kirkiri kafar, a San Francisco, da ke jihar California ta Amurka.

Sai dai an kaddamar da ita a watan Yulin shekarar.

Kididdiga da aka samu a watan Mayun 2015 ta nuna cewa fiye da mutane miliyan 500 suna amfani da Twitter kuma sama 332 suna amfani da kafar sosai.

Ana dai rubuta da aike sakon da bai wuce kalmomi 140 ba ta kafar ta Twitter.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Fiye da mutane miliyan 500 na amfani da Twitter.

Kafofin watsa labarai da kamfanoni da 'yan kasuwa da 'yan siyasa dama gwamnatoci suna sahun farko wajen amfani da kafar ta Twitter.

Sai dai kuma za a iya cewa matasa ne suka fi yin amfani da kafar.

Shin ko wace rawa kafar sada zumuntar ta Twitter ta taka a rayuwarka?