Hanyoyin da shafin Twitter ya sauya rayuwar al'umma a shekaru goma da fara shi

Image caption Sumita Dalmia ta hadu da mijinta Anuj a shafin Twitter.

Shekaru goma bayan da Jack Dorsey ya kaddamar da shafin twitter, da kalaman nan da ke cewa "just setting up my twitter", watau "yanzun na bude shafin twitter", shafin muhawarar ya shiga rayuwar miliyoyin al'ummar duniya, inda har ya sauya rayuwar wasu ma.

Daga inda aka yi amfani da harrufa 140, wajen neman aure, zuwa ga inda aka tsumo juyin juya-hali daga dan tsokacin mutum guda da ke zaune bisa kujerar gidansa, jama'a sun yi ta bayar da labarai iri-iri domin nuna murnar zagayowar shekaru goma ana amfani da shafin na twitter.

Baiko na farko ta shafin Twitter
Image caption An yi auren Stephanie da Greg Rewis a shekarar 2009 bayan ya yi tambayar ta a shafin Twitter.

A lokacin da wani dan Amurka mai suna Greg Rewis ke tunanin wata hanya ta daban da zai nemi auren budurwarsa Stephanie, sai ya yanke shawarar cewa zai tambaye ta a shafin twitter, tunda a baya bata amince da tambayar ba lokacin da ya yi mata ta hanyar sakon kar ta kwana.

"Kamar da wasa aka faro shi" Ya shaidawa BBC, ya kara da cewa, "Ina tattaunawa da Stephanie ta hanyar sakwannin kar ta kwana, inda nake tambayar ta ko zata aure ni, ita kuwa ta ce sai dai in mata tambayar ta wata hanyar daban."

"sai kawai na saka tambayar a shafin twitter, na kuma gaya mata ta duba. Kawai na ga ne kamar wannan lokacin shi ne daidai" In ji Greg.

Greg Ya kara da cewa, "Na yi matukar mamaki da na gano cewa wannan shi ne karo na farko da aka nemi aure ta shafin, sai lamarin ya kara bayar da ma'ana da sha'awa. Da na san da haka ai da na kara kawata komai"

Greg ya ce yanzu haka suna nan tare, amma dole ta sa suke kai kawo tsakanin garuruwan Phoenix da California, don haka suke yawan amfani da shafin twitter domin yin mu'amala, kazalika ya ce sun yi ta tura sakwanni a daidai lokacin bikinsu ta shafin.

"A shafin Twitter na gamu da Mijina"
Image caption Sumita Dalmia tayi mamaki matuka lokacin da saurayinta ya yi amfani da shafukan sada zumunta domin shirya tambayar aurensu.

Sumita Dalma, 'yar birnin Atlanta ce, wacce a 'yan shekarun da suka gabata ta lashe kyaututtukan da suka kai kimanin dala dubu 10, ta shafin twitter, a don haka ne ya sa 'yan uwa da abokan arziki basu yi mamaki ba da suka samu labarin ta samu masoyi ta shafin.

"Wata rana ina neman tikitin Jazzoo, wani biki da ake yi shekarar-shekara a garin Atlanta, a shafin," In ji Sumita

"Ina cikin nema, kawai sai ga sakon Anuj Patel ya fito- wanda shi ne yanzu aka min baiko da shi." Ta kara da cewa,

"Da har ya hakura da nasa tikitin, amma sai labarin rayuwarsa a shafin ya janyo hankalina, inda naga yana aiki sashen wasanni da nishadi ne, wajen da nake burin shiga. Kawai sai muka soma hira, muna tura sakwanni a twitter, sai muka koma sakwannin kar ta kwana, sai kuma waya, daga nan har muka hadu".

A watan Satumban shekarar 2013 sai Anuj ya shirya wata gagarumar liyafar tambaya, wadda ya sanya a shafin twitter.

Bayan Anuja ya sanya Sumita fasa lissafe-lissafe a shafin na twitter, da har ya kai ta har tsakiyar garin Atlanta, inda ta tarar ya na jiran ta a tsugune dauke da kwalin twittar da ya rubuta tambayar aurenta.

Matasa sun shiga a dama dasu kan lamarin siyasar Biritaniya
Hakkin mallakar hoto Twitter Abby Tomlinson
Image caption Yanzu Abby Tomlinsonna shirin karatu a fannin siyasa a jami'a.

Lokacin zaben Biritaniya a shekarar 2015, wata matashiya 'yar shekara 18 mai suna Abby Tomlinson daga Mersyside, ta kirkiro wani maudu'i mai suna #Milifandom, wanda ya taimaka wajen janyo hankalin jama'a kan rashin mutunta jagoran jam'iyyar Labour, Ed Miliband da 'yan jarida suka yi.

"Na yanke shawarar shiga siyasar dumu-dumu saboda kaunar da nake wa Ed Miliband" In ji Abby.

Cikin lokaci kalilan wannan maudu'i ya farin jinin zama na daya a Biritaniya, inda ya fito da magoya bayan Miliband a fili.

Bai dai taimake shi ga cimma nasarar ba, amma ya sauya rayuwar Abby.

Abby ta yi bayanin cewa washe gari manema labarai suka neme ta, inda ta yi hira da su, kuma ta yi wasu rubuce-rubuce a jaridu, ta kara da cewa bayan 'yan makonni shi Ed da kansa ya yiwo waya ya mata godiya.

Ta ce, "Zan iya cewa shafin twitter ya sauya mun rayuwata, saboda ya taimaka min gane inda na dosa da abunda nake son yi a rayuwa."

"Na samu aiki ta shafin twitter"
Image caption Marwa Mammoon ta yi amfani da shafin Twitter, inda ta samu aiki bayan boren da aka gudanar a Misra a shekarar 2011.

Marwa Mammoon 'yar asalin kasar Masar ce kuma ma'aikaciyar BBC ce, amma a shekarar 2011 sai ta koma zaman gida.

Ganin cewa tana da juna biyu, baza ta samu shiga zanga-zangar da ake gudanarwa lokacin da aka yi bore a Masar ba, sai ta bude shafin twitter, wanda hakan ya sauya mata rayuwa.

"Gani dai zaune a gida, amma nayi dumu-dumu cikin siyasa". In ji ta.

Ta kara da cewa, "Sai in zabi wata muhawara duk mako, kamar kaciyar mata ko cin zarafin mata da sauran matsalolin da matan da ke yankunan Larabawa ke fama da shi, in yi rubutu a kai".

"Ban yi la'akari da irin jama'ar da ke sauraro na ba, kawai hidima ta nake. Kafin in sani, sai naga ana kira na daya daga cikin matan Laraba mafi daukaka a twitter".

Marwa ta ce washe gari sai duk jam'iyyun siyasan Masar suka fara neman ta da ta shiga jam'iyyarsu. Ta ce duk da bata da isasshen kudi bata amince ba, sai ta tura sakon barkwanci ta twitter, cewa tana neman aiki.

Ban yi aikin jarida ba, na yi aiki ne a fannin kasuwanci, amma sai ga shi na samu aiki a matsayin edita na wani shafin jarida ta intanet na kamfanin wasu Amurkawa.

Shafin ya yi nasarar sosai, inda daga bisani kuma Marwa ta koma aiki da Majalisar Dinkin Duniya, sannan kuma ta koma Radio Netherlands, daga nan kuma ta soma aiki da BBC.