Ranar tunawa da Wa'ke ta duniya

Hakkin mallakar hoto MEHR
Image caption Yau ce ranar wa'ke ta duniya

Yau ce Ranar Wa'ke ta Duniya, wacce hukumar raya al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya, UNESCO, ta ware don bunkasa harsuna ta hanyar wake.

Manufar ranar dai ita ce karfafa wa al'umma gwiwar komawa ga al'adunsu na yin wa'ke da kuma kawata fasahar wa'ken.

A cewar UNESCO dai, wake ne kashin bayan adabin baka wanda tun kaka-da-kakanni yake sadar da kyawawan al'adun al'ummomi daban-daban.

Albarkacin wannan rana, wakilinmu na Kano Yusuf Ibrahim Yakasai ya zanta da Malam Garba Gashua Kano, wani marubucin wake.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti