Ana bikin ranar ruwa ta duniya

Image caption Ranar 22 ga watan Maris na kowacce shekara rana ce da a kan yi bikin ranar ruwa ta duniya

Ranar 22 ga watan Maris ta kowacce shekara rana ce da a kan yi bikin Ranar Ruwa ta Duniya da nufin wayar da kan al'umma game da muhimmancin amfani da tsaftataccen ruwan sha.

Wasu alkaluma da kungiyar WaterAid Nigeria mai fafutukar ganin an samar da tsaftataccen ruwan sha suka bayyana sun nuna cewa har yanzu kusan kashi daya cikin uku na al'ummar Najeriya na fuskantar matsalar rashin ruwa mai tsafta.

Kungiyar ta kuma ce rashin ruwa da muhalli mai tsafta na haddasa mutuwar yaran da ba su kai shekara biyar ba su dubu sittin da takwas a duk shekara a kasar.

A shekarar 1993 ne majalisar dinkin duniya ta kebe ranar 22 ga watan Maris a matsayin ranar ruwa ta duniya, inda aka yi bikin ranar na farko.