Zambia: An tsare jagoran jam'iyyar adawa

Image caption Shugaban kasar Zambia, Edgar Lungu.

Jami'an tsaro sun kama jagoran jam'iyyar adawa ta Zambia, bisa zarginsa da bata sunan shugaban kasar, Edgar Lungu.

'Yan sanda sun ce Eric Chanda, wanda ke jam'iyyar Fourth Revolution, ya yi wa Mista Lungu zargi na kazafi a kan wani hutu da ya dauka jim kadan bayan rantsar da shi.

A farkon wannan watan ne dai, aka kama wani babban mamban jam'iyyar adawa ta UPND, bisa zarginsa da laifin bai wa 'yan tawaye horo a sirrance.

'Yan adawa sun ce gwamnatin kasar na neman tsorata su ne kawai, gabannin zaben da za a gudanar a watan Agusta mai zuwa.