'Yadda na kusa zama 'yar kunar bakin wake'

Ranar Talata 9 ga watan Fabrairu, wasu 'yan mata guda biyu sun shiga sansanin 'yan gudun hijira da ke garin Dikwa na jihar Borno, a arewa maso gabashin kasar.

Mintuna kalilan da shigar su, suka tayar da bama-baman da ke jikinsu, suka kashe mutane 58.

Yarinya ta uku ta ki zama 'yar kunar bakin wake kamar yadda 'yan kungiyar Boko haram suka bukace ta ta yi.

Hauwa, ba sunanta na gaskiya ba kenan, ba ta san shekarunta ba, amma da alama za ta kai shekara 17 ko 18.

Ta shafe fiye da shekara guda tsare a hannun 'yan kungiyar Boko Haram, kuma suka bukace ta da ta kai harin kunar bakin wake Dikwa.

'yan kungiyar sun shaida wa 'yan matan uku cewa, idan suka kai harin, za su shiga aljanna.

Sai dai Hauwa ta ki amincewa da hakan.

'Iskokai'

Hauwa ta shaida wa BBC ta bakin tafinta cewa: "Na ce a'a, tunda mahaifiya ta tana zaune ne a sansanin 'yan gudun hijira da ke Dikwa, ba zan je in kashe mutane ba. Na gwammace in je in zauna da iyali na, ko da kuwa zan matu a can."

Iyayenta da 'yan uwanta na zaune ne a sansanin 'yan gudun hijirar da ke Dikwa, in banda dan uwanta daya da ya shiga kungiyar Boko Haram.

Sansanin 'yan gudun hijrar na Dikwa dai na kunshe da mutane kimanin 50,000.

Image caption Dubban mutane ne ke samun mafaka a sansanin gudun hijira na Dikwa

Hauwa ta yi wa BBC karin bayanin yadda ta kare a hannun 'yan Boko Haram.

"Ina da matsalar iskokai, a don haka 'yan Boko Haram suka ce min za su taimaka mini wajen kawar da iskokan."

Ba mu san hakikannin rashin lafiyar da Hauwa ke fama da ita ba, sai dai ta ce 'iskokan' da ke damunta, idan suka motsa, ta kan yi fitsari ko kashi a jikinta ba ta sani ba, sannan a baya ma har hannunta ta kona a wuta.

Ko ma mecece matsalar ta, ta ce ta ga alamar samun waraka a wajen 'yan Boko Haram, a don haka ta bi su.

Ta tuna yadda rayruwar ta ke kasancewa karkashin 'yan Boko Haram.

"Muna zaune ne a gidajen zana. A lokacin da miji na yana nan, ina girki sau uku a rana...mazan kan sato nama su kawo mana mu dafa."

Bayan wani lokaci, Hauwa ta rabu da mijinta, ta sake wani auren.

Mijinta na biyu ya tsere daga cikin 'yan Boko Haram din, a don haka suka bukace ta da ta sake aure na uku, amma ta ki.

A don haka suka bayyana mata bukatar su:

"Suka ce tunda na ki sake aure, to sai in dau bam in je in yi kunar bakin wake," in ji ta.

Image caption Hauwa ta ce, "Suka ce tunda na ki aure to sai na je na yi kunar bakin wake."

Sansanin 'yan gudun hijira da ke Dikwa, na kimanin kilomita 85 daga Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Hauwa ta san sansanin sosai, kuma ba shi da nisa daga inda 'yan Boko Haram ke tsare da ita, a don haka ta sulale kafin gari ya waye a ranar da ake son ta kai harin kunar bakin wake a Dikwa.

Ta ce ta yi nufin ta ankarar da iyayenta da sauran mutanen da ke zaune a sansanin 'yan gudun hijirar da ke Dikwa cewa ana shirin kai musu harin kunar bakin wake.

Sai dai ta makara.

Domin tuni 'yan kunar bakin wake biyu suka tayar da bam dinsu kafin ta karasa Dikwa.

Wani jami'ain soja ya nuna wa tawagar BBC inda aka kai harin.

"Nan ne inda bam din farko ya tashi", in ji shi yana nuna mana alamun jinin da ya fara bacewa a kan kwalta.

Titin ne dai ya raba bangarori biyu na sansanin 'yan gudun hijirar, a don haka, dole ne su tsallaka ta wajen da harin ya auku, domin su debo ruwa ko kuma su karbo abinci.

Har yanzu akwai kimanin mutane 15,000 da ke zaune a sansanin, kuma sun bayyana cewa suna tsoro.

Sai dai ba su da wani wajen da ya fi tsaro za su je, a don haka suke ci gaba da zama a sansanin.

A yanzu sun ce ba su yarda da kowa ba, har yara ma sun zame musu abin tsoro.

Wata dattijuwa mai suna Falmata Mohammed, ta tuna lokacin da harin kunar bakin waken ya faru.

Image caption Falmata Muhammad

"Wani soja na kokarin ya gyara mana layin da muka yi na karbar abinci da dibar ruwa .... Sai ga wata mata, tana sanye da jan Khimar, tana kuma da gashi mai tsawo."

Falmata ta ce, ta juya a lokacin da ta ji matar tana korafi a kan sojojin, a lokacin da suke kokarin tarwatsa mutanen da ke kan layin.

"Muna matsawa kan kwalta, sai ta yi ihu 'wayyo', tana kukan cewa cikinta yana ciwo... Mutane sun ruga domin taimaka mata, su daga ta sama, a lokacin ne ta tashi bam din da ke jikinta. "

"Kawai sai muka ga wuta ta tashi", in ji ta, a lokacin ne ta ga gawawwakin mutane warwatse a kewaye da ita.

Hauwa ba ta nan lokacin da aka kai harin, amma an nuna mata hatunan mutanen da harin ya shafa, kuma ta bayyana ra'ayinta game da makomar sauran 'yan matan da suka kai harin.

"Hotunan ba kyan gani. Ba abu ne mai kyau ba mutum ya dauki bam, ya je ya kashe mutane," in ji ta.

"Ban sani ba ko sauran 'yan matan sun san cewa za su mutu idan suka kai harin kunar bakin waken."

Iyaye a yankin na arewa maso gabashin Najeriya, na bayyana tsoronsu ga aikace-aikacen Boko Haram.

Domin kungiyar a shirye take, ta sace 'ya'yansu, ta kuma turo su su kashe iyayen nasu a inda suke samun mafaka.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mayakan Boko Haram sun sha kai hare-hare da dama a arewa maso gabashin Nigeria

A dai jihar Bornon ne kungiyar Boko Haram ta sace 'yan mata fiye da dari biyu daga garin Chibok a watan Aprilun shekarar 2014. Har yanzu ba a gano su ba.

Ita dai Hauwa, ta yanke shawarar bijirew 'yan kungiyar Boko Haram, ta kuma tsere daga hannunsu, ta hakan ta tseratar da rayuwar ta da sauran mutane da dama.

Mun tattauna da ita game da burinta na rayuwa, inda ta ce: "ina son in yi karatu.