Blackberry ya koka kan matakin Facebook

Hakkin mallakar hoto Reuters

Kamfanin wayar Blackberry ya bayyana taikaci dangane da matakin da shafin sada zumunta na Facebook ya dauka na daina samar da dandalinsa ga masu amfani da wayoyi kirar Blackberry.

Wannan mataki yana nufin cewa, masu amfani da wayar Blackberry ba zasu samu dandalin Facebook da aka tanada domin masu amfani da Blackberry ba.

Koda a farkon wannan watan WhasApp wanda mallakar kamfanin Facebook ne ya ce, masu amfani da wayar Blackberry Priv mai dauke da manhajar Android ne kadai zasu iya amfani da shi.

Kamfanin Blackberry ya koka da cewa, ya yi iyakar kokarinsa domin ganin cewar, ya tafi tare da Facebook da WhatsApp amma hakan bai sauya komai ba.

Sai dai Facebook bai ce uffan ba dangane da wannan batu.