Bama-bamai sun fashe a filin jirgin Brussels

Image caption Ranar Juma'ar da ta gabata ne dai jami'an tsaron Belgium da na Fransa suka kama Salah Abdeslam.

Bama-bamai guda biyu sun fashe a filin jirgin sama na Zaventem da ke birnin Brussels, a Belgium.

An ce dai bama-baman sun tashi a wurin da matafiya suke zama kafin su hau jirgi.

Jami'an kwana-kwana sun fadawa kafafen watsa labaran kasar cewa, an rasa rayuka da dama da kuma jikkata sakamakon fashewar bama-baman.

Har wa yau, rahotanni na cewa wasu bama-baman sun tashi a filin jirgin kasa na Maelbeek da ke birnin na Brussels.

Sai dai kuma har yanzu, ba a iya tantance hakikanin dalilin tashin bama-baman ba.

Wannan dai yana zuwa ne kwanaki hudu, bayan kama Salah Abdeslam, a Brussels din, wanda ake zargi da kitsa hare-haren da aka kai a Paris na Faransa, a watan Nuwamba.