Brussels: An wallafa hoton wadanda ake zargi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Fasinjoji sun shiga rudani bayan tashin bama-baman.

'Yan sanda a Belgium suna gudanar da bincike a fadin kasar, bayan hare haren bama-bamai a babban birnin kasar Brussels, wadanda suka yi sanadiyar mutuwar fiye da mutane 30, da raunata wasu da dama.

'Yan sandan sun fitar da hoton wani mutun da suke nema ruwa a jallo, bisa zargin sa da hannu a harin na filin jirgin sama na Zaventem.

Wani mai shigar da kara na gwamnati, Frederic Van Leeuw, ya ce 'yan kunar bakin wake biyu sun mutu a hare-haren, amma suna neman mutun na uku ruwa a jallo.

Kungiyar IS ta ce ita ke da alhakin kai hare-haren.

Gwamnatin Belgium din ta sanar da zaman makoki na kawa uku a fadin kasar.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yadda gilasai suka tarwatse sakamakon tashin bama-baman.

Da misalin 7:00 agogon GMT ne dai bama-bamai guda biyu suka tashi a wurin da masu jiran hawa jirgi suke zaman jira, a filin jirgin Zaventum.

Sai kuma wani bom din na uku, wanda ya tashi a wata tashar jirgin kasa ta karkashin kasa a Brussels din.

Image caption 'Yan sanda sun kama Salah Abdeslam.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne jami'an tsaron Belgium bisa hadin gwiwar na Faransa suka kaddamar da wani samame a birnin na Brussels wanda kuma ya kai ga cafke Salah Abdeslam, mutumin da ake zargi da kitsa hare-haren ta'addanci a birnin Paris na Faransa.

Aranar 13 ga watan Nuwamba ne dai aka kai hare-haren a birnin na Paris, al'amarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 120.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ma'aikatan agaji suna taimakawa wajen daukar wadanda harin ya shafa.

Tun lokacin ne ake zargin cewa Salah Abdeslam ya buya a birnin na Brussels.

Yanzu haka dai shugabannin turai sun fara kiraye-kirayen tsaurara matakan tsaro a kasashen nahiyar tare da dunkulewa wuri daya wajen ganin bayan abin da suka bayyana da ta'addanci.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jami'an tsaro suna zagaya birnin Brussels.

An dai baza jami'an tsaro kuma suna bincike gida-gida da sako-sako na birnin.