Kai Tsaye: Fashewar bama-bamai a Brussels

Latsa nan domin sabunta bayanai

Bama-bamai sun tashi a filayen jirgin sama da na kasa da ke Brussels na kasar Belgium kuma rahotanni na cewa an rasa rayuka da dama. Ku kasance da mu domin samun bayanai da dumi-duminsu dangane da al'amarin.

3:21 An fito da tawul-tawul daga hotel domin amfani da su wajen tsayar da jinin da wadanda suka jikkata suke zubarwa.

Hakkin mallakar hoto Getty

3:05 Firaiministan Birtaniya, David Cameroon ya ce an tabbatar da mutuwar dan birtaniya guda a hare-haren na Brussels.

Hakkin mallakar hoto epa

3:03 Rahotanni dai sun ce bam din ya tashi a tashar ta jirgin kasa, jim kadan bayan barin jirgin tashar.

Hakkin mallakar hoto No credit

2:58 Mutane 20 ne suka mutu sakamakon tashin bam din a tashar jirgin kasa.

Hakkin mallakar hoto Getty

2:49 Rahotanni na cewa kididdigar mutanen da suka rasa ransu a harin na bam sun kai 31.

Hakkin mallakar hoto AP

2:22 'Yan sanda sun sami wata riga ta bam wadda ba ta tashi ba.

Hakkin mallakar hoto AP

2:09 Shugaban Faransa, Francoise Hollande ya yi AllaH wadai da hare-haren, a inda ya ce dole ne kasashen turai su hada karfi da karfe wajen gano 'yan ta'adda da kuma yaki da su.

2:05 Bidiyon fasinjoji a lokacin da suke ta kansu, bayan tashin bama-baman, a filin jirgin saman na Zaventum da ke Brussels.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

2:00 Wannan dai shi ne karo na biyu da Belgium take fuskantar irin wannan yanayi, tun bayan harin da aka kai a birnin Paris na Faransa. A lokacin ne Belgium ta tsaurara matakan tsaro.

1:42 Al'ummar kasar Belgium dai suna cikin halin dimuwa. an umarci mutane da su tsaya a cikin gidajensu. Ma'aikata su kasance a ofisoshinsu sannan kuma 'yan makaranta su cigaba da zama a ajujuwansu.

1:18 Yanzu haka 'yan sanda Belgium suna bi gida-gida da lungu da sako suna bincike domin gano masu hannu a hare-haren.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Hakkin mallakar hoto Getty Images

1:15 Rahotanni sun ce an samu bindiga kirar Kalashnikov a wurin da bama-baman suka tashi.

1:12 Sabbin alkalumma sun nuna cewa kawo yanzu mutane 26 ne suka mutum sannan 136 suka jikkata sakamakon hare-haren bam a Brussels.

12:21 An yi kasa-kasa da tutocin tarayyar turai domin nuna alhini dangane da abun da ya faru.

Hakkin mallakar hoto Getty

11:48 Za a fito da jami'an tsaro 1,600 domin sanya ido a kasar Faransa sakamakon abun da ya faru a Brussels.

11:46 Kawo yanzu dai babu wani mutum ko kungiya da ya dauki alhakin kai hare-haren. To amma masu goyon bayan kungiyar IS ta kafafen sada zumunta sun bayyana farin cikinsu dangane da harin.

11:42 Mai magana da yawun hukumar kwana-kwana, Pierre Meys ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa akalla mutane 23 ne suka mutu sakamakon hare-haren.

Hakkin mallakar hoto Reuters

11:32 Mai shigar da kara na gwamnati ya shaidawa kafar watsa labaran kasar cewa tashin bama-baman, harin kunar bakin wake ne.

11:27 Hoton fasinjoji a yanayin dimuwa, jim kadan bayan tashin bama-bamai, a filin jirgin saman Zaventum.

Hakkin mallakar hoto Getty

11:18 An kuma baza jami'an tsaro domin sanya ido da bincike ko za a iya gane wanda ke da hannu a tashin bama-baman.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Hakkin mallakar hoto

11:16 Gwamnatin Belgium ta umarcin 'yan kasar da ka sance masu kula da abin da ka iya jewa ya zo dangane da tashin bama-baman.

11:13 Wasu fasinjoji sun ce kafin fashewar bama-baman a filin jirgin na Zaventum, sai da suka ji karar harbe-harbe.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

11:10 Rahotanni na cewa an tsaurara matakan tsaro a filin jirgin Gatwick da ke birnin London

11:06 Rahotanni na cewa yanzu haka fashewar bama-baman a Brussels ya janyo tsaurara matakan tsaro a filayen jiragen sama da ke nahiyar turai.

Hakkin mallakar hoto Getty

11:03 Bayan kuma wani dan lokaci sai aka samun rahoton fashewar wani bam din a tashar jirgin kasa ta Maalbreek wadda take kusa da ginin Tarayyar Turai.

Hakkin mallakar hoto Getty

11:01 Da misalin karfe 7:00 agogon GMT ne dai bama-bamai guda biyu suka tashi a filin jirgin saman Zaventum na Brussels.

10:52 Ana dai zargin Salah Abdeslam da kitsa harin da aka kai birnin na Paris ranar 13 ga watan Nuwamba wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 120.

10:50 A ranar Juma'ar da ta gabata ne dai 'yan sandan kasar ta Belgium bisa hadin gwiwar 'yan sanda Faransa suka kai wani samame, a inda suka yi nasarar cafke Salah Abdeslam wanda ake zargi da kitsa hare-haren ta'addanci a birnin Paris na Fransa.

10:42 Sai dai kuma wasu na ganin ba zai rasa nasaba da hare-haren ta'addanci ba.

10:40 Har yanzu dai ba a iya tantance hakikanin dalilin tashin bama-baman ba.

10:37 Yanzu haka, tuni aka kwashe mutane daga filayen kuma an tsayar tashi da saukar jirage.

Hakkin mallakar hoto Getty

10:30 Fasinjoji dai sun samu kansu a halin dimuwa sakamakon tashin bama-baman.

Hakkin mallakar hoto Getty

10:29 Har wa yau, rahotanni na cewa wasu bama-baman sun tashi a filin jirgin kasa na Maelbeek da ke birnin na Brussels.

Hakkin mallakar hoto Getty

10:22 An ce dai bama-baman guda biyu sun tashi a wurin da matafiya suke zama kafin su hau jirgi.

Hakkin mallakar hoto Getty
Hakkin mallakar hoto Getty

10:10 Akalla mutane 13 ne suka rasa rayukansu sakamakon fashewar bama-bamai a filin jirgin sama da tashar jirgin kasa da ke Brussels, babban birnin Belgium.

Hakkin mallakar hoto AP