Buhari ya yi Allah-wadai da harin Brussels

Hakkin mallakar hoto Nigeria Government
Image caption A baya-bayan nan Buhari ya gana da shugabannin kasashe da dama don yakar ta'addanci

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bi sahun shugabannin kasashen duniya wajen yin tir da hare-haren da aka kai filin jirgin sama da tashar jirgin kasa a Brussels.

Shugaba Buhari ya mika sakon jajensa ga firai minista Charles Michel, da daukacin al'ummar Belgium kan mutuwar mutane 30 da suka mutu a hare-haren.

Ya kuma tabbatarwa da kasar Belgium cewa Najeriya na tare da su a wannan hali na jimami.

A wata sanarwa da ta fito daga fadarsa, shugaba Buhari ya ce wadannan hare-hare da aka kai Belgium, na nufin akwai bukatar kasashen duniya su kara hada karfi da karfe don magance matsalar ta'addanci da murkushe masu yin sa.

Ya kuma bayar da tabbacin cewa Najeriya za ta ci gaba da aiki da sauran kasashen duniya don tabbatar da cewa an murkushe ayyukan ta'addanci.

A ranar Talata ne aka kai hare-haren bama-bamai guda biyu birnin Brussels na kasar Belgium.

Karin bayani