"Za mu zartar da kasafin kudi a makon nan"

Image caption Tun watanni uku da suka gabata ake sa ran majalisa za ta zartar da kasafin kudin

'Yan majalisar dattawan Najeriya sun ce suna sa ran majalisar za ta zartar da kasafin kudin shekarar 2016 cikin makon nan.

Tun watanni uku da suka gabata ake sa ran majalisar za ta zartarda kasafin, amma sai aka samu jinkiri sakamakon bitarsa da aka yi ta yi saboda faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya.

Shugaban majalisar dattawan kasar Sanata Bukola Saraki ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa majalisar za ta tabbatar da cewa ta zartar da kasfin kudin kafin karshen makon nan.

Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudin da ba a taba yin irinsa ba, na kimanin dala biliyan 30 a watan Disambar 2015.

Sai dai bayan wata guda ya nemi da a janye kasafin domin yin sauye-sauye sakamakon faduwar da farshin man fetur ya sake yi a duniya.

"Karin kudin ruwa"
Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Babban bankin Najeriya ya kara kudin ruwa daga kashi 11 cikin 100 zuwa kashi 12 cikin 100

A gefe daya kuma, kwamitin tsare-tsaren manufofin kudi na Najeriya ya ce ya kara kudin ruwa daga kashi 11 cikin 100 zuwa kashi 12 cikin 100.

Kwamitin ya bayyana haka ne a taron da ya yi ranar Talata karkashin jagorancin shugaban babban bankin kasar, Godwin Emefiele.

Kwamitin ya kuma yi kira ga gwamnatin kasar a kan ta zartar da kasafin kudin bana ba tare da bata lokaci ba, don samun walwalar kudade a tattalin arzikin kasar.