Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Bangaren lafiya na bukatar bincike

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan Najeriya dai na korafi akan tabarbarewar bangaren lafiya a kasar.

A 'yan shekarun nan, bangaren kiwon lafiya na Najeriya na fama da matsaloli da dama, wadanda ke neman durkusar da shi.

Matsalolin sun kama daga karancin liktoci zuwa ga rashin kwararrun ma'aikatan lafiya, da lalacewar asibitoci zuwa ga rashin kayan aiki, da wasu matsalolin da dama, wadanda suka haddasa yawan tafiye-tafiyen da 'yan kasar ke yi zuwa kasashen waje don neman lafiya.

Wani babban likita mai suna Dr Hassan Ibrahim ya ce babbar matsalar da bangaren lafiya ke fuskanta shi ne likitocin bogi da aka fi kira da Sojan gona, ga abinda ya shidawa BBC.