Niger: ''Yan adawa ku bi a hankali kan sakamako"

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaban Jamhuriyar Niger, Mahamadou Issoufou, karo na biyu.

A jamhuriyar Nijar wasu 'yan kungiyoyin fararen hula, da ma 'yan siyasa, suna ci gaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da matakin da 'yan hamayyar kasar suka dauka, na kin amincewa da sakamakon zaben shugaban kasar.

'Yan farar hular na ganin lamarin na iya jefa kasar cikin wata gurbacewar siyasa idan ba a yi hankali ba.

Shugaban jamhuriyar Niger, Mahamadou Issoufou ya samu nasarar zarcewa a kan karagar mulkin kasar, bayan da ya kayar da abokin takararsa, Hama Amadou.

Hukumar zabe ta jamhuriyar Nijar CENI ce dai, ta sanar da cewa shugaba Muhammadou Issoufou ne ya lashe zaben kasar bayan kammala tattara sakamako.

CENI ta ce shugaba Issoufou ya lashe zaben ne da kashi 92.5 cikin 100, yayin da abokin karawarsa Hama Amadou ya samu kashi 7.4 cikin 100.

Wannan dai shi ne karo na biyu da shugaban zai yi mulkin kasar.

Sai dai kuma tun kafin a bayyana sakamakon zaben, gamayyar jam'iyyun adawa masu goyon bayan Hama Amadou ta watsi da sakamakon bisa zargin magudi.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Shugaba Issoufou ya yi jawabi jim kadan bayan da hukumar CENI ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben, inda ya bayyana farin cikinsa.