Cuba: 'Yan Republican sun soki Obama

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Obama tare da Raul Castro a lokacin ziyarar kasar Cuba.

Shugaba Obama na Amurka na kammala ziyarar da yake yi a kasar Cuba, ranar talata, inda zai gana da 'yan aware, daga bisani kuma ya gabatar da wani jawabi da za a watsa a telebijin din kasar.

Yayin ziyarar, Mista Obama ya bayyan kare hakkokin bani Adam da kyautata harkokin siyasa da muhimman abubuwan da zai dukufa akai a tsibirin.

Sai dai kuma masu neman takarar shugabanci Amurka na jam'iyyar Republican sun caccaki ziyarar shugaban zuwa Cuba.

Donal Trump ya koka cewa Shugaban Cuba Raul Castro bai karbi bakwanci Shugaba Obama ba, a filin jirgin sama abin da ya kira da rashin mutunta kasar Amurka da Castro ya yi.

Shi kuma Ted Cruz wanda dan asalin Cuba ne ya ce fadar "White House" ta goyi bayan mulkin kama-karya, da kuma mulkin rashawa da daniyya suka dabaibayeshi.

Shi kuwa John Kasich ya zargi Barack Obama da yawaita ba wa kasar Cuba wasu fa'idodi da suka shige kima, ba tare kuma da ita kasar Cuba ta sakawa Amurkar ba.