Za a hukunta yaro mai harbi a Amurka

'Yan sanda na kokarin kama dan bindiga Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ba wannan ne karo na farko da akai harbi irin wannan ba.

'Yan sanda a Amurka sun ce ya kamata a hukunta yaron nan dan shekaru hudu da ya harbi mahaifiyarsa yayin da suke tafiya acikin mota.

Mahaifiyar yaron Jamie Gilt ta ajiye bindigar da take makil da harsashi a karkashin kujerar direba a motar, amma da tafiya tayi tafiya sai bindigar ta gangaro zuwa kujerar bayan direba inda danta yake zaune. Ya dau bindigar ya harbe ta ta baya.

Ya zuwa yanzu dai ba a san halin da take ciki ba.

'Yan sanda dai suna so ne a tuhume ta da barin bindigar har ta kai ga yaro karami.