An gano dan jihadi a harin Brussels

'Yan uwan juna da suka kai hari Brussels Hakkin mallakar hoto
Image caption An gano daya daga cikin hamaran na da alaka da harin da aka kai Paris a bara.

Jami'an Faransa da na Belgium sun ce daya daga cikin 'yan kunar bakin waken da suka kai harin ranar Talata a birnin Brussels yana da hannu a hada bam din da aka yi amfani da shi wajen kai harin watan Nuwambar bara a birnin Paris.

Jami'an sun ce, kwayoyin halitta na DNA da aka dauka daga jikin Najim Lashrawi daya suke da wadanda aka samu a jikin wata riga da aka makalawa bam a lokacin harin birnin Paris.

Yanzu dai ta bayyana cewa, ba wasu ne kawai suke kai su ba bisa radin kansu ba, aiki ne na wasu da suke da tsari shiryayye.

Kwamishinan harkokin cikin gida na kungiyar tarayyar Turai yace, akwai karancin amincewa juna tsakanin kasashen Turai, kuma hakan na takaita musayar bayanan tsaro a tsakaninsu.

Dimitris Avromopolous ya fadawa BBC cewa tilas kasashen Turai su yi aiki tare domin kaucewa sake aukuwar hari kamar wanda aka kai a birnin Brussesl.