Abubuwa 5 da za ku yi don samun kariya yayin hari

Abubuwa 5 da za ku yi don samun kariya yayin hari

Bama-bamai uku ne suka tashi a Brussels babban birnin kasar Belgium, inda mutane fiye da 30 suka mutu kuma da dama suka jikkata.

An kai biyu daga cikin hare-haren ne filin jirgin sama na Zavebtem, bayan sa'a daya kuma sai wani bam din ya tashi a babbar tashar jirgin kasa ta Brussels.

Wani shafin intanet mai alaka da kungiyar IS ya ce kungiyar ce ta kai hare-haren.

BBC ta yi duba kan abubuwa biyar da za ku iya yi don samun kariya idan ka samu kanka a wajen da aka kai irin wannan hari.

Hakkin mallakar hoto
Image caption Belgita kara zama cikin shirin ko ta kwana
"Ka zamo cikin shiri"

Da yawa daga cikin mutane da suke filin jirgi na Zaventem ba su san abin yi ba lokacin da suka ji karar tashin bam din a wajen, zun zaci wani gwaji ne kawai.

Kwararru a harkar tsaro sun ce lokacin da za ka iya dauka don fahimtar me yake faruwa na iya zama na mutuwa.

Amma idan har akwai wanda ya yi tunanin wani mummunan abu na iya faruwa, to shi zai fi kowa hanzarin sanin me yake ciki.

Wani masanin halayyar dan adam kuma mai horaswa kan ceton rai a harkar soji, John Leach, ya ce, "Babban abin da ka ke bukatar yi shi ne tunanin shin idan wani mummunan abu ya faru, me ya kamata ka fara yi."

Yana da kyau ka san inda hanyoyin tserewa na gaggawa suke a filin jirigin, ko na wani gini da ka ziyarta ko ma na ginin wajen da ka ke aiki.

"Yi hanzari ku kuma taimaki juna"

Masana halayyar dan adam sun ce yawancin mutane za su dimauce su rasa abin yi yayin da aka kai hari. Amma hanzarin yin wani abu na iya sa wa mutum ya tsira da ransa. Amma halayyar dan adam ce ya jira sai ya ga abin da sauran mutane suka yi kafin ya san abin yi.

Wani masanin halayyar dan adam kuma kwararre a sanin dabi'ar hayaniyar mutane Chris Cocking, ya ce, hada kai da sauran jama'ar da ke wajen na iya sa mutane su samu hanyar tsira.

Haka kuwa wani ma'aikacin kamfanin jirgin daukar kaya na Swissport, Anthony ya yi a ranar Talata.

Tsakaninsa da inda bam din farko ya tashi mita 20 ne kawai. Ya shaida wa gidan talbijin na Faransa cewa, "Kowa ya fara gudu ta kai-ta kai a wajen. Sai na yi tsalle a kan himilin kayan da ke gabana na tsuguna kasa."

Shi da wasu mutane biyu suka buya a bangaren da ake shigewa da kaya. Ya ce, "Tsoronmu daya ne kawai, idan suka sauko inda muka buya, to mun san kashinmu ya bushe."

A yayin da suke wannan boyo sai Anthony ya kira lambobin gaggawa har sau biyu. An umarce su da su ci gaba da buya. Ya roki 'yan sanda su zo su dauke shi da abokan buyarsa, amma hakan bai samu ba. Don haka sai suka yanke shawarar tserewa inda suka yi ta ta tsakankanin kaya.

Ya ce, "A wannan lokaci ne muka ga wani ma'aikacin DHL wanda ya dauke mu ya nuna mana hanyar da za mu bi mu fita. Ba mu sani ba ma ko dan ta'adda ne cikin kayan aikin DHL, amma dai ba ya dauke da wani makami.... Ya kai mu har bakin kofar fita wajen da jirgi ke tsayawa, inda ma'aikatan DHL ne kawai suke bi."

"Yi kokarin ganin ranka bai salwanta ba"

Masu bayar da shawara kan tsaro sun ce, ka yi kokarin ganin ka samu hanyar tsira don ganin baka rasa ranka ba. Wannan na iya hadawa da durkusawa kasa ko kuma buya a bayan wani abu. Idan ma buyan ne to samu bayan katanga ka labe ko wani abu mai kwari.

Idan aka kai hari a matsattsen waje to harsashi daya kacal na iya ji wa mutane da dama ciwo. Amma idan ka buya ba lallai ne kai harsashin ko kuma tartsatsin wuta ya sameka ba.

Kazalika, ka kwanta ka yi bakam kamar ka mutu na iya sa wa ka tsira da ranka, yayin da a wasu lokutan kuwa gudu na iya zama shi ne kadai hanyar tsirarka.

Gwamnatin Biritaniya ta bayar da shawarar yin gudu in har akwai hanyar yin hakan. Amma idan babu, to buya shi ne mafi a'ala.

An kira irin wannan hanya a matsayin "gudu, da buya da kuma fada."

Hakkin mallakar hoto
Image caption An ayyana makokin kwana uku a Belgium
"Mayar da martani"

Yin kukan kura kan dan bindiga ya yi aiki a wasu yanayin. A watan Agustan shekarar da ta gabata, wani al'amari ya faru a jirgin kasa a Faransa, bayan da fasinjoji suka fi karfin wani dan bindiga da ya shiga jirgin.

Amma daga cikin fasinjoji hudun da suka yi masa rubdugu, daya daga cikinsu sojin sama ne dayan kuma dogarin da yake tsaron fadar shugaban kasa ne.

Su ne kadai mutanen da suka yi hobbasa wajen kwace bindigar mutumin.

Wani tsohon sojan Biritaniya Ian Reed, ya ce ba abu ne mai kyau ba ka tinkari dan ta'adda ba tare da ka samu horo ba.

Ya kara da cea, "Yin hakan kasada ce da sa rayuwa cikin hatsari."

Yana da kyau ka tuna cewa mahara da dama na aiki ne karkashin tawaga. Wasu za su daura bam a jikinsu yayin da wasu za su dauki makamai a hannunsu.

Duk da irin hadarin da ke akwai, wasu mutanen na ganin cewa yana da muhimmanci ka shirya jan daga idan ta kama.

"Bayan tsira"
Hakkin mallakar hoto AFP

Da zarar mutum ya samu ya tsira, to kamata ya yi ya kokarta sa ido da zama cikin shiri sosai kuma.

Mista Reed ya ce, "Ka yi nesa sosai da wajen, ka labe a maboyar da za ta baka kariya sosai ka kuma je wajen hukuma mafi kusa don neman taimako."

Akwai hadari ka shiga cikin cincirindon mutane da ke kusa ko kuma ka shiga motar haya.

Ya kara da cewa, "ko da yaushe ka dinga ganin kamar akwai wani babban abin da ka iya sake biyo baya."

Babban abu mai muhimmanci dai shi ne daukar shawarar 'yan sanda ko sauran jami'an tsaro, saboda za su fi sanin ainihin yadda lamarin yake.