Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

'Yan adawa za su iya daukaka kara

Image caption 'Yan adawa sun kauracewa zabe zagaye na biyu.

A jamhuriyar Nijar, masana na ci gaba da tsokaci kan matakin da 'yan adawar kasar suka dauka na cewa ba zasu yi biyayya ga gwamnatin Shugba Muhamadou Issoufou ba.

'Yan adawar dai sun ce daga ranar daya ga watan Afirilu, watau ranar da wa'adin shugaban kasar na farko zai cika, su a saninsu babu wata gwanmnati a kasar, domin a cewarsu ba a gudanar da zabe yadda yakamata ba, da ya bai wa shugaban wa'adin mulki na biyu.

A ranar Talata ce dai hukumar zaben kasar watau CENI ta bayyana shugaban kasar a matsayin wanda ya lashe zaben kasar zagaye na biyu, wanda 'yan adawa suka kaurace masa bisa zargin magudi da kuma tsare dan takararsu Hama Amadou a gidan yari.

Malam Mustapha Kadi, wani jagoran kungiyoyin farar hula ne, kana mai sharhi kan lamuran siyasa, ya yi wa BBC karin bayani kan ko 'yan adawar na da ikon kin amincewa da gwamnatin kasar.