Za a tono gawarwakin fursunonin Afrika ta Kudu

Hakkin mallakar hoto b
Image caption Nelson Mandela shi ne shugaban gwagwarmayar neman 'yanci lokacin mulkin wariyar launin fata
Ma'aikatar shari'a ta kasar Afirka ta Kudu, ta ce za a tono gawarwakin wasu fursunonin siyasa 83 da aka kashe ta hanyar ratayewa tun a zamanin mulkin nuna wariya a kasar.

An binne gawarwakin ne a wasu wurare a gidan kaso, wanda a da ake kira gidan yarin Pretoria.

Bayan an tono gawarwakin, za a tantance ko su wanene, sannan a mika su ga iyalansu domin su sake binne su.

Akasarin fursunonin, mambobin kungiyoyin gwagwarmayar neman 'yanci ne, na Africanist Congress da United Democratic Front, wadanda kamar kungiyar African National Congress ta Nelson Mandela, suke adawa da mulkin turawa.

Tuni dai aka riga aka tono gawarwakin wasu fursunonin siyasan 47 da aka kashe su su ma ta hanyar ratayewa.