Brussels: An gano 'yan kunar bakin wake

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Har yanzu ba gano mutum na uku ba

Kafafen yada labaran kasar Belgium sun ambato wasu matasa 'yan uwan juna, Khalid da Ibrahim el-Bakraoui, a matsayin 'yan kunar bakin wake guda biyun da suka kai hari, a babban filin jirgin sama na Zaventum da tashar jirgin kasa da ke Brussels na kasar Belgium.

Kafar ta ce Ibrahim ne ya kai harin filin jirgin saman Zaventum wanda kuma ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 14.

Yayin da shi kuma Khalid ya tayar da nasa bam din a tashar jirgin karkashin kas, a inda mutane kusan 20 suka rasa rayukansu.

Akalla mutane 240 suka jikkata sakamakon fashewar bama-bamai a wuraren biyu, ranar Talata.

Kungiyar IS ta dauki alhakin kai harin.

Kasar ta Belgium dai ta ayyana kwanaki uku domin alhinin abin da ya faru.