'Yan adawa sun yi sulhu a Syria

'Yan tawaye na kabilar Houthi

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Akallah mutane 6000 aka hallaka a rikicin na Yemen.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce banagarori biyu da ke rikici da juna a Yemen sun amince su tsagaita wuta a ranar 10 ga watan gobe.

Ya yin da aka sanya ranar 18 watan a matsatin ranar da za a fara tattaunawar sulhu a kasar Kuwait, dan kawo karshen zubda jinin da aka kwashe shekara guda ana yi a kasar.

A baya dai tattaunawa irin wannan ta fuskanci turjiya, ya yin da manzo na musamman na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Yemen Isma'il Ould Cheikh yace dakatar da bude wuta da tattaunawar su ne dama ta karshe da aake da ita da za ta kawo karshen yakin da ake yi a kasar.

An yi kiyasin akalla mutane 6000 ne suka rasa rayukansu a yakin da kawancen da Saudiyya ke jagoranta su ke yi da 'yan Shi'a na kabilar Houthi da Iran ke marawa baya.