Kamaru: Fursunoni sun sake mutuwa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Biya

Wasu fursunoni uku sun sake mutuwa daga cikin wadanda suka jikkata a boren gidan yarin birnin Garoua a Kamaru, a ranar 13 ga watan maris.

Har yanzu kuma, akwai wasu fursunoni fiye da 10 da suke samun kula a asibiti.

Kusan fursunoni 80 ne da aka yanke wa hukunci, aka mayar da su gidan yarin ladabtarwa na Tchollire.

Sakamakon binciken da Hukumar kare hakkokin bil adam ta Kamaru ta gudanar na bayyana cewa fursunoni 8160 ne suke zaune a gidajen yarin arewacin kasar, alhalin kuma adadin wuraren zama ba su fice 4000 ba.

Hakan ya jawo tsananin zafi, ya gallabi fursunoni, al'amarin da ya sa suka tayar da bore.