Kamaru : Masu amfani da Intanet sun karu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption hanyar sadarwa na zamani

Sakamakon wani binciken da kamfanin Kaymu mai cinikin kayayyakin sadarwa na zamani a yanar gizo ya wallafa, ya nuna cewa mutane miliyan 2.5 ne suke amfani da Intanet.

Kazalika, sakamakon ya nuna cewa kashi 11 na daukacin al'ummar ne suke amfani da wannan hanyar sadarwa.

Kashi 20 na matasa masu shekara 18 zuwa 24 a duniya sune suka fi shahara wurin yin amfani da Intanet.

A yayin da uku ne kacal na dattawa masu sama da shekaru 65 a duniya su ne a sahun karshe.

Binciken kuma ya karkare da cewa maza na sahun gaba wurin yin amfani da Intanet fiye da mata.