An fara yunkurin kwato Mossoul

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption sojojin iraki

Kasar Iraki ta ce dakarunta sun kai farmaki na farko domin su samu kwato birnin Mossoul wanda kungiyar IS ta mamaye shekaru biyu da suka gabata.

Wata sanarwar jami'an soji ta ce, dakarun Irakin sun fatattaki magoya bayan kungiyar zuwa wajen gari tare da hadin gwiwar sojojin sama na Amurka.

Masana sun ce har yanzu babu wata alamar cewa dakarun kurdawa na Peshmergas na da hannu a cikin wannan farmakin.

Hakazalika dakarun Iraki sun sanar da cewa farmaki makamanta a baya can wadannan a baya ba su yi tasiri ba.

Birnin Mossoul wanda yake kunshe da mutane kusan miliyan biyu ya zama mafi girma da kungiyar IS ta mallaka a Iraki ko kuma Syria.