Boko Haram ta fitar da wani sabon bidiyo

Hakkin mallakar hoto AFP

A Nigeria, kungiyar Boko Haram ta fitar da wani sabon bidiyo wanda ke nuna shugabanta, Abubakar Shekau yana raye.

Bidiyon wanda ya kai tsawon kusan mintuna takwas ya nuna shugaban kungiyar, Shekau a wani yananyi na rashin kuzari, idan a kwatanta da sauran bidiyon da ya fito a baya.

Shekau yana zaune ne da kayan sojoji a jikinsa kuma akwai bindiga a jingine a kafadarsa ta hagu.

A bidiyon, shugaban kungiyar dai ya yi magana da harshen Larabci da kuma Hausa.

Ya mika gaisuwa ga mayakansa tare da shaida musu cewa ya fitar da sabon bidiyon saboda ya tabbatar musu cewar yana raye.

Abubakar Shekau ya jima bai fito a bidiyon kungiyar ba, tun bayan da kungiyar ta yi mubaya'a da kungiyar ISIS a shekarar 2015.

A baya dai sojojin Najeriyar sun sha ikirarin cewa sun kashe Shekau.