Mutane 5 sun mutu a Niger

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wannan abu ya faru ne kwanaki kadan da kammala zabukan kasar

<span >Rahotanni daga jamhuriyar Nijar sun ce mutane 5 sun mutu wasu da dama suka ji rauni, sakamakon fasahewar wani abu da ake kyautata zaton wata na'ura ce ta masu aikin hakar zinare.

Al'amarin ya faru ne a wani gida da ya zama matattarar 'yan ci rani a garin Agadez.

Tuni dai 'yan sanda suka killace wajen, yayin da aka kai marasa lafiyar kuma asibiti.

Ga Tchima Illa Issoufou da karin bayani:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti