Nigeria za ta yi nazari kan kasafin kudi

Hakkin mallakar hoto Nigeria Senate
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta yi nazari a kan kasafin kudin kasar da 'yan majalisar dokoki suka amince da shi.

A ranar Laraba ne dai majalisun na dattawa da ta wakilai suka amince da kudurin kasafin kudin da kwamitoci masu kula da shi suka mika musu, bayan an jima ana jira.

Wannan dai shi ne kasafin kudi na farko da wannan gwamnati tayi.

Honourable Abdurrahman Kawu Sumaila, shi ne babban mataimaki na musamman ga Shugaba Muhammadu Buhari a kan al'amuran majalisar Wakilai, kuma ya shaida wa Bilkisu Babangida yadda fadar shugaban kasar ta ji da amincewa da kudurin kasafin kudin:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

A watan Disamba ne shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin a gaban majalisa na naira tiriliyan shida da biliyan 77 da miliyan 680, kwatankwacin dala biliyan 30, amma ya nemi da a janye shi bayan wata daya don yin gyare-gyare, sakamakon faduwar farashin man fetur. Yawan kudin dai bai sauya ba amma gibin kasafin ya karu da naira tiriliyan uku daga naira tirilyan 2.2.