Jagoran Sabiyawa zai sha dauri

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Iyalan wadanda lamarin ya shafa kenan dauke da kyallaye da aka yi rubutu a kai, a gaban kotun lokacin da ake gudanar da shari'ar.

An yankewa tsohon jagoran Sabiyawan Bosnia, Radovan Karadžić, daurin shekaru 40 a gidan kaso bayan da aka same shi da laifin kisan kare dangi da kuma muggan laifukan kan bil adama a lokacin yakin Bosnia a shekarun 1990.

Wata kotun MDD a Hague ta yanke hukuncin cewa Mr Karadžić ne ke da alhakin kisan kiyashin da aka yi a Srebrenica, inda aka yi wa maza manya da yara su dubu 8 kisan gilla.

Alkalin kotun O-Gon Kwon, ya bayyana laifukan da aka same shi da aikatawa, inda ya ce ya ga wani shiri na dai daita lalata Musulman Bosnia da ke garin da gayya.

Lauyan Mr Karadzic dai ya ce zai daukaka kara.

Akalla mutane dubu dari ne suka mutu a lokacin rikicin, wanda ya jawo ballewar Yugoslavia.