Nigeria: An sace mata 16 a Adamawa

Abubakar Shekau Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan Boko Haram na yawan sace mata da kananan yara a Najeriya.

A Najeriya wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun sace wasu mata 16 a jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin kasar.

Lamarin ya faru ne a kusa da kauyen Sabon Garin Madagali da ke jihar Adamawa, tuni kuma jami'an tsaro suka bazama don bin sawun 'yan bindigar da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne.

Kamfanin Dillancin labarai na AFP ya rawaito kakakin 'yan sandan jihar Adamawa Usman Abubakar, ya tabbatar da sace 'yan matan, haka ma dan majalisa mai wakiltar yankin Adamu Kamale, ya shaida aukuwar lamarin.

Maharan sun sace matan ne a lokacin da suka tafi Daji don yin itace da kuma kamun kifi a wani rafi da ke kusa da kauyen, tare da rakiyar 'yan kato da gora biyu da suke taimakawa sojoji a yakin da su ke yi omian kawo karshen 'yan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Najeriya.