An kashe wata daliba a Bangladesh

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wannan ba shi ne karo na farko da ake zanga-zanga kan kisa a kasar ta Bangladesh ba.

Ana zanga-zanga a Bangladesh bayan kashe wata dalibar kwaleji, mai shekaru 19 a wani yanki dake da cikakken matakan tsaro na soji a kasar.

An gano gawar Sohagi Jahan Tonu ne a a cikin daji a garin Comila a daren Lahadi.

Har yanzu ba a fitar da sakamakon gwajin gano yadda aka yi ta mutu ba, amma ana ta yada cewa an yi ma ta fyade ne.

Masu zanga-zanga a makarantun kwaleji da wasu birane a fadin kasar, sun kakkafa shingaye ta hanyar, rike da hannayen juna, inda wasun su ke zargin 'yan sanda da yin rufa-rufa.