'Yan sandan Brussels sun kama mutane 6

'Yan sanda a bakin aiki Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jami'an tsaro na bincike gida-gida a Brussels dan gano wadanda ake zargi da hannu akai harin.

'Yan sanda a kasar Belgium sun kama mutane shida a ci gaba da samamen da suke kai wa bayan hare-haren da aka kai birnin Brussels da ya hallaka mutane sama da 30.

An yi kamen a ciki da wajen gundumomin birnin Brussels, da binciken kowanne gida a kokarin da suke yi na gano wadanda ake zargi da hannu a kai harin.

Sai dai 'yan sanda ba su bayyana sunayen wadanda suke tsare da su ba.

A bangare guda kuma jami'an tsaro sun gano wasu mutane biyu da ake zargin sun gudu bayan kai harin.

An dai gano su ne a hotunan internet tare da wanda ake zargi a filin jirgin sama da tashar jirgin kasa wuraren da bama-baman suka tashi.