Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

An kama mata 'yan kunar bakin wake a Kamaru

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jami'an tsaron sun kama matan ne a garin Limani.

Jami'an tsaro a Kamaru sun tabbatar da kama wasu 'yan mata biyu 'yan kunar bakin wake a garin Limani mai iyaka da Najeriya.

A yanzu haka 'yan matan na hannun jami'an tsaro a garin Mora inda ake ci gaba da yi musu tambayoyi.

Sai dai kuma mai magana da yawun ma'aikatar tsaro Kanar Didier Badjeck ya musanta cewa 'yan matan 'yan Chibok ne kamar yadda majiyoyi daban-daban suka yada.

Ga rahoton da Muhamman Babalala ya hada mana.