Nigeria da Egypt sun tashi wasa 1-1

'Yan wasan Super Eagles Hakkin mallakar hoto the nff twitter
Image caption An tashi wasan kunnen doki.

Najeriya da Masar sun tashi wasa kunnen doki 1-1 a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da suka kara a Kaduna ranar Juma’a.

Nigeria ce ta fara cin kwallon ta hannun Etebo Oghenekaro bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci.

Daf da za a tashi wasa ne Masar ta farke kwallon da aka zura mata ta hannun Mohamed Salah.

Da wannan sakamakon Masar tana mataki na daya a kan rukuni na bakwai da maki bakwai, yayin da Najeriya ke matsayi na biyu da maki biyar.

Najeriya za ta ziyarci Masar ranar Talata a wasa na biyu na neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a shekarar 2017.

Masar da Najeriya basu samu damar buga gasar cin kofin Afirka da aka yi a Equotorial Guinea a shekarar 2015 ba, wanda Ivory Coast ta lashe kofin.