Kano: Shaguna 3,500 sun kone —NEMA

Image caption Har yanzu ba a kai ga tantance iya hasarar da aka yi a gobarar ba.

Hukumar Agajin Gaggawa ta Nigeria NEMA ta ce, sama da shaguna 3,500 ne suka kone a gobarar kasuwar Sabon Gari a Kano.

A hirarsa da BBC Alhaji Sani Sidi Shugaban hukumar ya ce, gobarar ita ce mafi girma da aka taba yi a wata kasuwa a Nigeria.

Shugaban ya kuma kara da ya ce babu asarar rayuka, sai dai mutane 15 sun jikkata a gobarar, har yanzu ba su iya kididdige yawan dukiyar da aka yi hasara a gobarar ba.

Gobarar ta tashi ne a daren Juma'a, an kuma yi ta kokarin kasheta a ranar Asabar zuwa wayewar garin Lahadi.