Gobarar Sabon Gari ta lafa

Image caption Wasu daga cikin rumfunan da suka kone

An samu nasarar shawo kan gobarar da ta tashi a kasuwar Sabon Gari Kano, sai dai zuwa yammacin Asabar da akwai sauran wuraren da wutar ke ci.

Daruruwan shaguna ne suka kone kurmus, gine gine kuma suna ci gaba da riguje wa sabo da lalata su da wuta ta yi.

Hakkin mallakar hoto b
Image caption Motocin kashe gobara na kamfanoni sun taimaka wajen kashe gobarar

Wani jami'in lafiya ya ce sun kai sama da mutane 10 asibiti wadanda suka jikkata, sai dai har yanzu ba a kai ga samun rahoton rasa rai ba.

Tunda misalin karfe 12 na daren Juma'a gobarar ta tashi, amma har bayan karfe biyar na yammacin Asabar wutar na ci a wasu wuraren, ko da dai an ci karfin ta a mafi yawan wurare.

Image caption Shagunan da suka kone suna da yawa